May 17, 2025

Fadar Shugaban Ƙasa Ta Musanta Ikirarin Adesina Kan Halin da Najeriya Ke Ciki

0
images - 2025-05-05T055329.726

Daga Sabiu Abdullahi

Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta kalaman da aka danganta wa Shugaban Bankin Raya Afirka (AfDB), Akinwumi Adesina, inda ya bayyana cewa halin da Najeriya ke ciki yanzu ya fi muni fiye da na shekarar 1960.

Mai ba Shugaban Ƙasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya wallafa a shafinsa na X cewa Adesina ya dogara da ƙididdigar da ba su dace da sahihan bayanan da gwamnati ke da su ba.

A cewar Onanuga, “Babu mai hangen nesa da zai ce Najeriya ba ta samu ci gaba ba tun bayan samun ‘yancin kai. Duk da cewa muna jiran sabon tsarin ƙididdigar GDP daga Hukumar NBS, za mu iya cewa tattalin arzikin ƙasar ya ninka na shekarar 1960 sau 50 ko fiye.

“Ya ci gaba da sukar Adesina, yana cewa ya yi jawabi “kamar ɗan takarar siyasa irin su Peter Obi, ba tare da cikakken bincike ko tabbaci daga sahihan hanyoyi ba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *