November 8, 2025

Faɗa ya ɓarke tsakanin sojoji da ƴan kasuwa a kasuwar Banex da ke Abuja

images-4-7.jpeg


Daga Sabiu Abdullahi

Wani rikici da ya barke tsakanin sojoji da ‘yan kasuwa a kasuwar Banex da ke Abuja ya kai ga tura jami’an leken asiri na rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya.

Wani faifan bidiyo ya nuna fararen hular da suna fafatawa da sojojin a ranar Asabar.

Rikicin dai ya samo asali ne sakamakon takaddamar sayar da wayar salula, a cewar wani dan kasuwa mai suna Abdul.

“Matsalar ta faro ne a lokacin da wasu sojoji suka zo korafin wayar, kuma rigima da ‘yan kasuwa ya kai ga fada.” Inji Abdul.

Hedikwatar tsaro da mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Onyema Nwachukwu, ba a samu jin ta bakinsu ba.

Sai dai ofishin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ya tabbatar da cewa kwamishinan ‘yan sandan, Benett Igweh, ya aike da tawagar ‘yan sandan farin kaya zuwa wurin da lamarin ya faru.

A halin yanzu dai ana gudanar da bincike kan lamarin, kuma ana kokarin ganin an dawo da zaman lafiya a yankin.

1 thought on “Faɗa ya ɓarke tsakanin sojoji da ƴan kasuwa a kasuwar Banex da ke Abuja

  1. Doess your blog have a ontact page? I’m hazving problems locating iit but,
    I’d like to send youu aan email. I’ve got somme ideas ffor yor blog you might bbe
    interersted inn hearing. Either way, great blog and I look
    forweard too seeig it expand over time.

Comments are closed.