March 28, 2025

Elrufa’i Ya Ce Ba Don Muƙami Ya Goya Wa Tinubu Baya Ba a 2023

images-2025-02-11T111230.767.jpeg

Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa goyon bayan da ya bai wa Shugaba Bola Tinubu a zaben 2023 ya kasance ne bisa kyakkyawar niyya, ba don neman mukami ba.

A ‘yan kwanakin nan, El-Rufai ya samu sabani da wasu jami’an gwamnatin Tinubu, lamarin da ya samo asali bayan ya soki jam’iyyar APC mai mulki kan abin da ya kira “sauya alkibla daga manufofinta.”

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, El-Rufai ya jaddada cewa aikinsa yana bisa ka’ida da gaskiya, ba don wata manufa ta kashin kai ko tsammanin lada ba.

“Mun yi abin da muka yi domin Allah, kasa, da jam’iyya, ba tare da fatan samun wani sakamako a madadinsa ba. Abin da ke faruwa a yanzu wani darasi ne daga rayuwa da kuma halayyar dan Adam,” in ji jigon APC.

1 thought on “Elrufa’i Ya Ce Ba Don Muƙami Ya Goya Wa Tinubu Baya Ba a 2023

Comments are closed.