January 15, 2025

El-Rufai ya maida martani kan bincikensa da ake yi

0
IMG-20240606-WA0024.jpg

Daga Abdullahi I Adam

Tirka-tirkar siyasa ta sake kunno kai a jihar Kaduna inda tsohon gwamnan jihar Mal. Nasir Elrufa’i ya zargi cewa binciken da ake shirin yi masa a jihar bita-da-ƙulli ne na siyasa mare tushe ballantana makama.

A wata sanarwa da Muyiwa Adekeye wanda shi ne mai magana da yawun tsohon gwamnan ya fitar a jiya Laraba, ya ce binciken da ake wa Elrufa’in bai da tushe kuma tsohon gwamnan “ya mulki Kaduna da gaskiya.”

A jiya ne dai majalisar jihar ta Kaduna ta sanar da cigaba da binciken tsohon gwamnan tare da miƙa kwafin binciken ga ɓangaren zartaswa domin ɗaukan matakan da su ka kamata, kamar yadda kakakin majalisar Hon. Yusuf Limam ya sanar.

Majalisar ta fara binciken Elrufa’in ne tun watan Afrilu kan zargin sama da faɗi da wasu maƙudan kuɗaɗe tare da amfani da dukiyar jihar ba bisa ƙa’ida ba wanda Elrufa’in ya sha musawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *