EFCC Ta Mika Wa Gwamnatin Tarayya Gidaje 753 Da Ta Ƙwace A Hannun Emefiele

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa, wato EFCC, ta mika gidaje 753 da ta ƙwato daga hannun tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ga Ma’aikatar Gidaje da Raya Birane ta Tarayya.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede ne ya mika takardun mallakar gidajen ga Ministan Gidaje da Raya Birane, Ahmed Dangiwa, a wani taron da aka gudanar a yau Talata a Abuja.
Rahotanni sun nuna cewa wadannan gidaje, wadanda ba a kammala gina su ba, suna cikin gundumar Lokogoma da ke birnin tarayya Abuja.
A cikin wata sanarwa da Minista Dangiwa ya fitar, ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ne ya bayar da umarnin a kammala gine-ginen tare da sayar da su ga ‘yan Najeriya ta hanyar gaskiya da adalci.
Ministan ya ƙara da cewa ma’aikatarsa za ta tabbatar da cewa an kammala gine-ginen yadda ya dace domin su zamo ingantattun matsuguni da suka cika ƙa’idodin gine-gine na zamani.