January 15, 2025

EFCC ta kama tsohon gwamnan Taraba, Darius Ishaku, bisa zargin almundahanar naira biliyan 27

0
images (13) (23)

Daga Sabiu Abdullahi  

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta kama tsohon Gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku, bisa zargin almundahanar naira biliyan 27.  

A cewar wasu manyan majiyoyi a hukumar, an kama Ishaku ne a ranar Juma’a kuma yana ci gaba da tsare a hannun EFCC.  

Wata majiya ta bayyana cewa an gurfanar da Ishaku a kan akalla tuhume-tuhume 15, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu nan ba da dadewa ba, saboda an tattara shaidun da ake tuhumarsa a kai.  

Ishaku wanda dan jam’iyyar PDP ne ya taba rike mukamin gwamnan jihar Taraba daga watan Mayun 2015 zuwa Mayun 2023.   Wannan dai ba shi ne karon farko da gwamnatinsa ke fuskantar zargin cin hanci da rashawa ba.  

A watan Mayun 2021, Hukumar EFCC ta kama wasu jami’ai uku da suka yi aiki karkashin gwamnatinsa bisa zargin hannu a badɗakalar naira biliyan 21.  

Jami’an sun hada da sakatare na dindindin, Daraktan kudi da asusu, da mai karbar kudi a ma’aikatar kananan hukumomi da masarautu.  

Bincike ya nuna cewa ana fitar da wasu kudaden gwamnati da ake zargin an wawure a karkashin gwamnatin Ishaku daga asusun jihar ta hanyar cek na akalla naira miliyan 10 kowanne lokacin da za a cire kuɗi.  

Matakin na EFCC na daga cikin kokarin da take yi na magance cin hanci da rashawa da kuma tabbatar da bin diddigin al’amuran mulki a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *