June 14, 2025

EFCC Ta Kama Mutum 792 da Ake Zargi da Damfarar Kirifto a Lagos

FB_IMG_1734364002457.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Hukumar Yaki da Zambar Kudi ta EFCC ta kama mutane 792 da ake zargin suna damfara ta hanyar amfani da cryptocurrency a Lagos.

Mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, ya bayyana cewa wannan shi ne mafi girman adadin kama mutane a rana guda da hukumar ta taba yi.

An kama mutanen ne a wani gini mai hawa bakwai da ke Victoria Island a Lagos.

Uwujaren ya kara da cewa wadanda aka kama sun hada da Sinawa 114, Filifinawa 40, Kazartawa biyu, dan kasar Pakistan guda daya, da kuma dan kasar Indonesiya guda daya.

15 thoughts on “EFCC Ta Kama Mutum 792 da Ake Zargi da Damfarar Kirifto a Lagos

Comments are closed.