May 17, 2025

EFCC Ta Kama Chanisawa Da Ƴan Najeriya Bisa Zargin Fitar Da Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba

FB_IMG_1731083832830.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Najeriya, EFCC, ta kama wasu ’yan kasar Sin guda biyu, Wang Jiang da Wang Richard, tare da wasu ’yan Najeriya guda biyu, Donatus Agupusi da Michael Benneth Agu, bisa zargin kokarin fitar da ma’adinai ba tare da izinin da ake bukata ba.

An kama Wang Jiang a filin jirgin sama na kasa da kasa na Akanu Ibiam da ke Enugu bayan an gano wasu duwatsu masu kama da ma’adinai a cikin kayansa.

An kama sauran mutanen a Ofishin EFCC na Shiyyar Enugu.

A cewar Dele Oyewale, shugaban sashen yada labarai na EFCC, bincike na farko ya nuna cewa Agupusi, mai kamfanin Great Wall Construction Limited, ne ya dauki sauran wadanda ake zargin aiki.

Jiang ya yi kokarin tafiya da ma’adinan zuwa kasar Sin domin gwaji ba tare da takardun izini ba.

EFCC za ta gurfanar da wadanda ake zargi a kotu da zarar an kammala bincike.