EFCC ta kama ɗan daudu Bobrisky saboda ‘cin mutuncin naira’
Daga Sabiu Abdullahi
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta kama wani dan daudu, Idris Okuneye, wanda aka fi sani da Bobrisky, bisa laifin lalata gami da cin zarafin Naira.
Kakakin EFCC, Dele Oyewale, a wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels, ya fada a ranar Alhamis cewa an kama Bobrisky ne a Legas a daren Laraba.
“An kama shi a daren Laraba a Legas,” in ji jami’in hukumar yaki da cin hanci da rashawa.
“An tsare shi a ofishinmu na Legas kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu.”
A halin yanzu dai ana ta magana a kan Bobrisky saboda dalilai daban-daban da suka hada da lashe lambar yabo ta “Mafi Iya Saka Sutura ta Mata.”