EFCC Ta Fara Bincike Kan Dala Miliyan 86 Da Aka Kama a Filin Jirgin Kano

Hukumar EFCC da ke yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya ta bayyana cewa ta fara bincike kan wani babban adadin kuɗin ƙasashen waje da aka kama a filin jirgin sama na Kano.
A cewar sanarwar da hukumar ta fitar, an kama dala $86,500,305 da kuma riyal 305,150 a cikin wata jaka da wani ma’aikacin filin jirgin, Sale Bala, ya yi yunƙurin ɗauka a ranar Lahadi.
“Binciken farko ya nuna cewa an ɓoye kuɗaɗen ne cikin zannuwan gado,” in ji sanarwar.
An kuma kama wani mutum mai suna Abdullahi Tahir, wanda ake zargi cewa shi ne aka shirya zai karɓi jakar bayan an kammala tantance ta.
EFCC ta ce tana tsare da kuɗaɗen tare da waɗanda ake zargin, kuma za ta gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala cikakken bincike.