January 15, 2025

Ecowas za ta kafa dakarun ko-ta-kwana don yaƙi da ta’addanci a yammacin Afirka

0
IMG-20240509-WA0013.jpg

Daga Sodiqat Aisha

Ƙungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka Ecowas ta ce za ta kafa dakarun ko-ta-kwana domin tunkarar matsalar ‘yan ta’adda masu iƙirarin jihadi da ke tayar da zaune tsaye a ƙasashe daban-daban, kamar yadda shafin intanet na The Nation mai zaman kansa a kasar nan ya rawaito.

Kwamishinan Ecowas Abdel-Fatau Musah ya fadi hakan ne jiya a Abuja cewa ƙungiyar na bukatar tara dala biliyan 2.4 ga dakarun, inda ƙasashe mambobin kungiyar suka bayar da rabin adadin.

Shugabannin sojojin Mali da Burkina Faso da Nijar dai sun janye daga kungiyar ta Ecowas a farkon wannan shekarar, bayan da suka zarge ta da rashin tallafa musu wajen tunkarar tashe-tashen hankula daga kungiyoyin al-Qaeda da IS a tsawon shekaru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *