January 14, 2025

Duk mai jin haushin shigata gwamnatin Tinubu ya je ya rungumi taransufoma—Wike

3
IMG-20240901-WA0010

Daga Abdullahi I. Adam

Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya bayyana cewa yana jin daɗin yin aiki da shugaban ƙasa Bola Tinubu da kuma gwamnatin jam’iyyar APC.

Wike, wanda jigo ne a jam’iyyar PDP, kuma ɗan adawa ɗaya tilo a majalisar ministocin Tinubu, ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a yayin taron jam’iyyar PDP a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.

Tsohon Gwamnan na Jihar Ribas ya bayyana cewa har yanzu bai haƙura da yin aiki da gwamnatin Tinubu ba, duk da sukar da ake masa bayan naɗin nasa.

A cewar ministan, bai yi nadama ba game da matakin da ya ɗauka, kuma ya gamsu da matsayinsa a gwamnati mai ci.

Wiken ya ce, “Muna cikin gwamnati. Muna cikin cikakkiyar gwamnatin Tinubu. Ba ni da nadama game da haka, kuma zan ci gaba da kasancewa a gwamnatin. Duk wanda ya fusata ya je ya rungumi taransfoma.”

Tun dai lokacin da aka naɗa Wiken matsayin Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja naɗin nasa ke haifar da tattaunawa, inda mutane da yawa ke nuna cewa matsayinsa na minista tukuici ne ga irin gudummawar da ya bayar wajen nasarar da Tinubu ya samu a Jihar Ribas a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

3 thoughts on “Duk mai jin haushin shigata gwamnatin Tinubu ya je ya rungumi taransufoma—Wike

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *