Duk da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta, Isra’ila Ta Ci Gaba da Kisan Gilla a Gaza

Daga Sabiu Abdullahi
Isra’ila ta ci gaba da kai hare-hare ta sama a Gaza gabanin fara yarjejeniyar tsagaita wuta da aka amince da ita tare da sakin waɗanda Hamas ke garkuwa da su. Ana sa ran yarjejeniyar za ta fara aiki ranar Lahadi, idan majalisar gudanarwar Isra’ila ta amince da ita.
Hukumar lafiya a Gaza ta bayyana cewa wasu hare-haren da Isra’ila ta kai jim kaɗan bayan amincewar yarjejeniyar a daren Alhamis sun yi sanadin mutuwar mutum 73. Cikin waɗannan akwai mutum 12 da suka mutu a wani gida da ke unguwar Sheikh Radwan, birnin Gaza.
A gefe guda, kafar BBC ta ambato cewa ma’aikatar tsaron Isra’ila ta yi bayanin cewa wani makami da aka gani ya faɗa a kudancin ƙasar a yau Alhamis, amma daga baya aka bayyana cewa kuskure ne.
Dakta Amjad Eliwah, wani likita a asibitin Baptist da ke birnin Gaza, ya shaida cewa ma’aikatan asibiti ba su samu hutun minti ɗaya ba cikin daren saboda cunkoson waɗanda suka jikkata. An ambato shi yana cewa, “An ci gaba da kawo waɗanda aka raunata, yayin da gawarwaki ake kaiwa kai-tsaye zuwa mutuware.”