DSS ta kama ƴan ƙasar Poland 7 da suka ɗaga tutocin Rasha lokacin zanga-zanga
Daga Sabiu Abdullahi
Hukumar tsaron farin kaya a Najeriya ta kama wasu ‘yan kasar Poland bakwai da suka ɗaga tutocin kasar Rasha yayin zanga-zangar kin jinin ƙudurorin gwamnati a jihar Kano da ke arewacin kasar.
Peter Afunanya, kakakin hukumar tsaro ta DSS, ne ya bayyana haka a wata sanarwa ranar Laraba.
Kamen dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar adawa da sauye-sauyen tattalin arzikin da shugaba Bola Tinubu ya kawo, inda kawo yanzu aka kashe mutane 22, kamar yadda kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta bayyana.
Afunanya ya ce an tsare ‘yan ƙasar ta Poland ne a lokacin da ake kokarin tabbatar da tsaro, amma bai bayar da cikakken bayani kan sunayensu ba.
Stanislaw Gulinski, karamin jakadan kasar Poland a Najeriya ya tabbatar da kamen, yana mai cewa an tsare su ne a Kano kuma suna cikin jirgin da zai kai su Abuja.
Ma’aikatar harkokin wajen Poland ta ce tana kokarin gano yanayin da lamarin ya faru da kuma tallafa wa ‘yan kasarta.
Zuwa yanzu dai ofishin jakadancin Rasha da ke Najeriya ya musanta cewa yana da hannu cikin ɗaga tutocin.
Masha Allah sabon gidan watsa labarai mai inganci da sabon hanyar sadarwa cikin salon zamani.