Dole Yahaya Bello ya fuskanci fushin doka—EFCC
Daga Sabiu Abdullahi
Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin almundahanar Naira biliyan 80, tabbas zai fuskanci fushin kotu.
Hukumar ta bayar da wannan tabbacin ne a lokacin da take mayar da martani ga al’ummar kasar dangane da rashin tafiyar da al’amarin tsohon gwamnan yadda ya kamata.
Wata sanarwa da kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya fitar a ranar Laraba, ta kuma bayyana dalilin da ya sa hukumar ta ki zuwa wurin tsohon gwamnan a lokacin da ya ziyarci hedikwatarta.
Ya kuma kara da cewa, inda ya dace ya mika kansa zai kasance a gaban mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Abuja, wanda a gabansa ne tawagar lauyoyinsa suka dauki nauyin gabatar da shi domin amsa tuhume-tuhume 18 na karkatar da kudade.
EFCC dai ta jima tana wasan Tom and Jerry da Yahaya Bello, wanda take ƙoƙarin kamawa.