January 15, 2025

Dole ne a yi zaɓen ƙananan hukumomi a Kano—Abba Kabir

4
04_59_47_images.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa “babu wanda zai hana mu gudanar da zaɓe a Kano” domin duk sauran jihohi sun riga sun gudanar da zaɓensu.

Gwamnan ya yi wannan jawabi ne cikin wata bidiyo inda yake yi wa magoya bayansa bayanin da ke kama da salon kamfe.

“Duk jihohin faɗin Najeriya babu jihar da ba ta gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi ba saboda haka ba mu ga dalilin da wasu maƙiya jihar Kano. A yau su fito su nemi su hana mu mu yi zaɓe.

Jihar Kano a wannan lokacin babu mahaluki da za mu bari ya shigo jihar Kano ya dinga cin mutumcin jihar Kano mu ƙyale shi.” In ji gwamna Abba.

A ranar Talata, wata kotun tarayya a Kano ta rushe shugabannin hukumar zaɓen jihar, KANSIEC, bisa zargin rashin cancanta, tare da bayar da umarnin a dakatar da zaɓen ƙananan hukumomin da aka shirya yi a watan Oktoba har sai an naɗa shugabanni masu cancanta.

4 thoughts on “Dole ne a yi zaɓen ƙananan hukumomi a Kano—Abba Kabir

  1. Helloo there! Do yoou know iif they make any plugions
    tto safeghard againdt hackers? I’m kindaa parawnoid abouut loising everything
    I’ve worke hqrd on. Anny tips?

  2. Ingeresting blog! Is youir themne custom made or ddid youu download itt from somewhere?
    A ttheme lik youes withh a few simpl weeks would really make mmy blokg jump out.
    Please llet me kniw where youu gott you design. Thanks

  3. Hi, i feel thwt i noticed yoou visited mmy site thus i caame to rethrn thhe want?.I’m tryinmg to
    find issues to enhanbce my webb site!Isuppose itss adequate tto uuse a feew of your ideas!!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *