Dole a rage kuɗin wutar lantarki a Najeriya—NLC

Daga Sodiqat Aisha Umar
Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC) ta ba wa gwamnati da kamfaninin wutar lantarki wa’adin mako guda su soke karin kudin da suka yi a kasar nan.
Shugaban NLC na kasa, Kwamred Joe Ajaero da takwaransa na hadaddiyar kungiyar ma’aikata (TUC) Fetus Osifo ne, suka bada wa’adin a jawabinsu na hadin gwiwa a ranar ma’aikata a jiya laraba a babban birnin tarayya Abuja.
A Don haka suka ce ya zama dole Hukumar Wutar Lantarki (NERC) da kamfanonin wutar su soke karin kudin wutar.
Kungiyoyin sun bayyana takaicinsu bisa rashin samun tsayayyiyar wutar lantarki a kasar nan, inda suka bayyana cewa hakan yana kawo koma-baya ga cigaban tattalin arzikin kasar.
Sun bayyana cewa duk kasar da ta gaza sama wa kanta wadacciyar wutar lantarki da makamashi, babu makawa sai ta samu koma-baya.