December 7, 2025

Dillalan man fetur sun ba wa gwamnatin Najeriya bas-bas masu amfani da gas

IMG-20240813-WA0012

Daga Sodiqat A’isha Umar

Shugaban Bola Tinubu ya karɓi motocin bas masu aiki da iskar gas, waɗanda ƙungiyar manyan dillalan man fetur ta Najeriya suka bai wa gwamnatin tarayya.

Ƙungiyar ta ce ta bayar da motocin bas ɗin ne a matsayin tata gudummawar wajen sauƙaƙa wa ‘yan Najeriya raɗaɗin da cire tallafin man fetur ya haifar.

Shugaban ƙungiyar ta Depots and Petroleum Products Marketers Association of Nigeria (DAPPMAN), Winifred Akpani, ya ce a cikin Najeriya aka harhaɗa motocin.