January 24, 2025

Dangote: Yanboko an ji kunya. Tir!, daga Dr. Aliyu Tilde

0
FB_IMG_1726384037298

Yau NNPCL ya fara daukan mai a matatar Dangote da ke Legas. Ga tarin injinmiyoyi da administrators (mahandama) na NNPC da matatun mai sai cin albashi da alawusai da suka fi na sauran ma’aikata na biliyoyin naira, amma a banza. Ko lita guda an gagara tacewa shekara da shekaru. Yau dankasuwa daya ya yi kuma dole kasa ta dogara da shi. NNPC ta zama yarjigila da yarkamasho.

Maciya amana sun samu rinjaye a gwannatocinmu tun bayan Murtala. Sun yi ta yi sai da suka durkusar da kasar ta kowane fanni. Yau ta kai cin-kacha da ake yi wa dukiyar mutane ya hana yiyuwar duk wani kamfanin gwamnati aiki. Hakanan ma’aikatu dabam dabam, sai y’an kalilan. Don haka dole a sake wa yankasuwa kusan komi.

Wannan cin amana shi ne dalilin tabarbarewar lamurra har yau ya kai ga tsaro ya koma tsoro. Talauci kuwa muddin ba rike amana aka yi ba, to yanzu aka fara. In ba amana kuma ba aminci, mu je zuwa.

Muna jinjinawa kalilan wadanda suke aiki tsakani da Allah a ma’aikatu, duk da kalubalen da suke fuskanta. Su sani Allah yana ganin aikinsu. Zai saka musu.

Shi kuwa Dangote muna masa tabarkalla. Ya fitar mana da kitse daga wuta. Yau za a ba shi danyen manmu, ya tace, ya biya mu da fetur, ya biya haraji a Naira, bukatar Dola ta ragu, matsin a kan Naira ya ragu, ta kara daraja, mu kuwa mu ci gaba da shan mai ba rashi. Wannan Bakanen, da ya yi halin zage-zagi da ya wuce nan ma. Kila ma da har sadaka zai rika yi da fetur din.

Allah ka sa mu ga karshen rashin tsaro kamar yadda muka ga karshen matsalar fetur, kuma ka sassauto mana farashinsa. Ita ma Dola ta yo kasa, Naira kuwa ta yi sama. Mu kuwa ka arzurtamu da rikon amana.

Dr. Aliyu U. Tilde

14 September 2024

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *