January 24, 2025

Dangote da Sanwo-Olu sun kai wa Tinubu ziyarar Sallah a Legas

0
20240616_143642-1024x683.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

A yau Lahadi ne shugaban kasa Bola Tinubu ya shirya wani taro na musamman domin bikin Eid-el-Kabir a gidansa da ke Legas.



Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi. 

Taron ya haɗa baƙi da suka haɗa da Mataimakin Gwamna Dokta Obafemi Hamzat, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Legas Dr. Mudashiru Obasa, Shugaban Ma’aikata na Jihar Legas Mista Bode Agoro, da Shahararren dan kasuwa Alhaji Aliko Dangote.

Sanwo-Olu ya bayyana cewa, “ A yau, na halarci wani taro na musamman na bikin Sallar Idi da aka yi a gidan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ke Legas.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *