December 7, 2025
image_editor_output_image935973147-1699005067650.jpg

Daga Dr. Aliyu Usman Tilde

Wani abu da Sarkin Musulmi, Sultan Sa’ad Abubakar ya kirkiro shi ne taron shekara shekara na aikace-aikacen Musulunci don tunawa da ayyukan da mujaddadi Shehu Usumanu Danfodiyo da sauran shugabannin jihadi suka yi.

Ayyukan sun hada da laccoci, kacici-kacici na makarantu, bayar da kyautukan girmamawa ga mutanen da suka yi fice a Najeriya kan harkar mulki, da karantarwa, da da’awa, dss.

Akan yi wannan aikin ne da hadin gwiwar kungiyar NACOMYO da wasu kungiyoyi bakwai ko fiye.

Taron bana ya kayatar kwarai. Na halarce shi da na bariya inda na ba da lacca a dukkansu. Abinda ya fi kayatar da ni shi ne gayyatar gwamnonin Kebbi da Zamfara da sarakunan Daular Usumaniyya ta Sokoto. Duk sun zo ko sun aiko da wakilansu. Nan gaba har na Daular Borno ya kamata a gayyata. Muna bukatar hadin kai yanzu fiye da kowane lokaci don cigaban Najeriya. Nan gaba har da sarakunan kudu, musulmi da kirista, ya kamata a gayyata don sada zumunci.

Gwamnonin da suka zo daga Kebbi da Zamfara (wanda ya turo matsi mataimakinsa) sun jaddada yabonsu da goyon bayan jama’arsu ga Sultan da jihadin da kakanninsa suka kaddamar a karni na 19 miladiyya. Haka nan sauran manyan baki.

Allah ka karawa Shehu Usumanu da dukkan malamai da mujahidan da suka jaddada musulunci da hada kanmu a zamaninsu. Allah ka ba mu ikon kwaikwayonsu gwargwadon iyawarmu. Allah ka ba masu da’awah da shugabanninmu zuciya da damar yi wa musulunci da kasarmu aiki saboda cigabanmu. Allah ka kara wa Annabi (SAW) da alayensa da sahabbansa gaba daya tsira da aminci. Amin. Amin.