Dan Majalisar Amurka Ya Zargi USAID da Ba da Tallafi ga Boko Haram da Sauran Kungiyoyin Ta’addanci

Dan majalisar wakilai na Amurka, Scott Perry, ya zargi Hukumar Raya Kasashe ta Duniya (USAID) da bayar da tallafi ga kungiyoyin ta’addanci, ciki har da Boko Haram.
Perry, wanda ke wakiltar Pennsylvania a jam’iyyar Republican, ya yi wannan zargi ne a ranar Alhamis yayin zaman farko na kwamitin da ke binciken yadda gwamnati ke aiwatar da ayyuka yadda ya kamata.
Kungiyar Boko Haram, wacce aka fi sani da Jamā’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihād, tana kai hare-hare a yankin arewa maso gabashin Najeriya da wasu kasashe makwabta kamar Chadi, Nijar, Kamaru da Mali. Kungiyar ta kashe dubban mutane tare da tilastawa miliyoyin mutane barin gidajensu cikin sama da shekaru 15 da suka gabata.
Zaman da aka yi wanda aka sanya wa suna “The War on Waste: Stamping Out the Scourge of Improper Payments and Fraud” ya mayar da hankali ne kan zargin yadda ake amfani da kudaden haraji.
Perry ya ce: “Wanene ke karɓar waɗannan kuɗaɗe? Shin sunan yana da wani tasiri a gare ku? Saboda kuɗin ku, kuɗin ku, dala miliyan 697 a kowace shekara, da kuma jigilar kuɗaɗen zuwa ga Madarassa, ISIS, Al-Qaeda, Boko Haram, ISIS Khorasan, sansanonin horar da ‘yan ta’adda – wadannan ne ake tallafa wa.”
Ya kuma bayyana damuwa kan yadda USAID ta ware dala miliyan 136 don gina makarantu 120 a Pakistan, amma ba a sami wata shaida da ke nuna an gina su ba.
“Kuna ba da tallafi ga ta’addanci, kuma [tallafin] yana fitowa ne daga USAID. Kuma ba kawai Afghanistan ba, har ma Pakistan da ke kusa.
“USAID ta kashe dala miliyan 840 a cikin shekaru 20 da suka gabata a shirin ilimi na Pakistan, ciki har da dala miliyan 136 don gina makarantu 120, amma babu wata shaida da ke nuna an gina su. Me yasa za a sami wata shaida? Domin mai binciken kwamitin bai iya shiga don dubawa ba.
“Amma kun san me ya faru? Mun ƙara kashe dala miliyan 20 daga USAID don kirkirar shirye-shiryen talabijin na ilimi ga yara da ba su iya zuwa makaranta. Amma ba za su iya zuwa ba, domin babu makarantun! Amma kuma kun biya kudin.
“Wani ya karɓi kudin. Kuna biya domin haɓakar ta’addanci. Wannan abin dole ne ya tsaya.”
Wadannan zarge-zarge sun biyo bayan umarnin tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, wanda ya nemi a rufe USAID saboda zargin cin hanci da rashawa.
Bugu da ƙari, attajiri Elon Musk, wanda aka naɗa don jagorantar Sashen Inganta Ayyukan Gwamnati, shima ya yi suka kan USAID, yana zargin hukumar da aikata ayyukan sirri.
Wadannan zarge-zargen da Perry da Musk suka yi sun haifar da cece-kuce kan yadda USAID ke kashe kuɗaɗenta da kuma yadda ake kula da ayyukanta. Har yanzu hukumar ba ta fitar da wata sanarwa kan wadannan zarge-zarge ba.
Instagram güvenlik cihazları 🌟 Büyük Kazançlar Sizi Bekliyor! FreeSpin ile Slotlarda Yüksek Ödüller Elde Edin! http://www.jadekusadasi.com/
I don’t knw iif it’s ust me orr if pperhaps everybody else experiencing issues with yor site.
It seemms like some oof thee written text on your
posts aree running ooff thhe screen. Can someone elsse pleaase comment annd let me knkw iif this is hqppening to thsm aas well?
Thhis coul be a issuee with my iternet broser becauuse I’ve had this hapen previously.
Thanks