June 14, 2025

Daliba Ta Yi Karyar An Sace Ta Inda Ta Nemi Miliyan Biyu a Matsayin Kudin Fansa

images - 2025-04-23T151103.871

Wata dalibar makarantar sakandare mai shekaru kimanin 16 ta shiga hannun hukumomi bayan da ta shirya karyar sace kanta tare da bukatar a biya kudin fansa har Naira milyan biyu domin a sako ta.

Rahotanni sun bayyana cewa dalibar, ‘yar ajin SS2 a wata makaranta mai zaman kanta da ke cikin birnin Abakaliki na jihar Ebonyi, ta nemi wani dan uwanta daga cikin iyalansu tare da shaida masa cewa an sace ta, sannan aka bukaci a biya kudin fansa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Ebonyi, Joshua Ukandu, ya bayyana wa manema labarai cewa binciken farko ya nuna cewa wani makusancin dalibar ne ya taimaka mata wajen tsara wannan karyar.

Duk da haka, rundunar ‘yan sandan ba ta bayyana sunan dalibar ko na makarantar da take karatu ba.Ukandu ya ce, “Har yanzu ‘yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken gaskiyar lamarin.”

Rundunar ta kuma bukaci iyaye da masu makarantu da su kula da tarbiyyar yara tare da karfafa musu muhimmancin gaskiya da amana.