Dakarun Najeriya sun ceto mutum 17 daga hannun ƴan bindiga
Dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadarin Daji sun ceto wasu mutane 17 da aka yi garkuwa da su a Jihar Kebbi tare da kwato babura daga hannun ‘yan bindiga a yayin wani aikin ceto.
An samu wannan nasarar ne a cikin daren ranar 12 ga watan Oktoban 2023 lokacin da dakarun Operation HADARIN DAJI da aka tura a Malekachi suka gudanar da aikin ceto sakamakon aiki da sahihan bayanai.
Sun samu labarin cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu da ba a tantance adadinsu ba a kauyen Kanya da ke karamar hukumar Danko- Wasagu ta jihar Kebbi inda suke kokarin tsallakawa da waɗanda suka sace zuwa Jihar Neja.
Dakarun sun yi gaggawar yin kwanton ɓauna a kan hanyoyin da ake zargin ‘yan bindigar za su yi amfani da su a kauyen Karenbana.
Bayan haka, sojojin sun nuna karfin iko inda suka tilasta wa ƴan bindigar yin watsi da wadanda suka sato tare da kashe wasu ‘yan bindigar, wasu kuma suka tsere da raunukan harbin bindiga.
Hakan ne ya yi sanadiyyar ceto mutane 17 da aka yi garkuwa da su ɗin.
Waɗanda aka ceto sun haɗa da mata 6 da maza 11 tare da wani ɗan sanda da aka yi garkuwa da shi a Danko-Wasagu.
An mika waɗanda aka ceto ɗin ga jami’an ƴan sanda na yankin Bena domin sada su da iyalansu.
Haka kuma sojoji sun kwato Babura 5 da aka ƙona a yayin farmakin.