January 15, 2025

DA DUMI-DUMI: Tinubu ya dakatar ministar jin ƙai Edu bisa zargin badakalar kudi

0
images-2024-01-08T143138.752.jpeg

By Sabiu Abdullahi

Shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Dakta Betta Edu, ministar harkokin jin kai da yaki da fatara, sakamakon binciken da ake yi kan zargin badakalar kudi.

A baya fadar shugaban kasa ta sanar da cewa, binciken ya ta’allaka ne kan badakalar naira biliyan 585.189 da minista Edu ta yi.

Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai da dabaru, ya tabbatar wa jama’a cewa za a dauki matakin da ya dace har sai an kammala binciken.

Takaddamar dai ta kunno kai ne yayin da rahotanni suka bayyana cewa an karkatar da kudaden da aka ware domin mabukata a jihohin Akwa Ibom, Cross River, Ogun, da Legas zuwa wani asusu na sirri.

Wannan tonon sililin ya janyo cece-ku-ce tsakanin jama’a tare da kara rura wutar bukatar korar Edu da kuma gurfanar da ita a gaban kuliya.

Wata takarda da aka bankado mai dauke da sa hannun Edu, ta yi cikakken bayani kan yadda aka fitar da naira miliyan 585.189 kai tsaye a cikin asusun sirri na Bridget Mojisola Oniyelu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *