Da ɗumi-ɗumi: Kotun Ƙoli ta yi watsi da buƙatar Atiku ta soke zaɓen Tinubu

Daga Sabiu Abdullahi
A ranar Alhamis ne kotun kolin kasar ta yi watsi da karar da aka shigar na neman soke zaben shugaba Tinubu kan zargin rashin bin sahihancin watsa sakamakon ta hanyar na’ura.
Korafin, wanda babban lauyan Atiku, Chris Uche, SAN, ya shigar, ya kunshi dalilai 35 na daukaka kara.
Daga cikin batutuwan da aka kalubalanta sun hada da hukuncin da kotun ta yanke kan watsa sakamakon ta hanyar lantarki, cancantar Tinubu a zaben, da kuma damuwa kan kuri’un babban birnin tarayya.
Sai dai a hukuncin da kotun kolin ta yanke, ta fayyace muhimman batutuwan da suka shafi shari’ar.
Kotun ta jaddada cewa ko da tsarin kallon sakamako mai zaman kansa (IREV) ya gaza, ba zai dakatar da tattara sakamakon ba.
Bugu da ƙari, rashin aiki na IREV ba ya rage amincewar masu jefa ƙuri’a a cikin tsarin zaɓe.
Da yake zartar da hukuncin, Mai shari’a Okoro ya bayyana cewa, “A bisa wadannan dalilai, an yi watsi da bukatar kuma an ki amincewa.”