Da ɗumi-ɗumi: Jirgin sojin sama ya faɗo a Kaduna
Daga Abdullahi I. Adam
Wani jirgi mai saukar ungulu na rundunar sojin Najeriya ta sama ya faɗo a safiyar yau Litini a ƙauyen Tami na ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna.
Waɗanda lamarin ya auku a kan idonsu sun tabbatar da cewa jirgin ya faɗo ne misalin ƙarfe 5:00 na asuba, wanda ya zame wani abin firgici ga mazauna wajen.
Ana hasashen cewa jirgin ya gamu da tangarɗar na’ura ne daidai lokacin da yake shawagi a sama wanda hakan yai sanadiyyan faɗowansa, amma dai matuƙin jirgin ya tsira da ransa bayan faruwar lamarin.
Shedu sun tabbatar ma TCR Hausa cewa jama’an garin sun kawo ɗauki cikin gaggawa wanda hakan ya kawo jin daɗi ganin cewa ba’a sami asaran rayuka ba.
“Mun ji wani ƙara mai tada hankali, sai mu ka fita da gaggawa domin kai ɗauki, amma mun ji daɗi ganin cewa matuƙin bai rasa ransa ba” inji mutanen garin.
Tuni jami’an rundunar sojin saman ta aike da dakaru inda lamarin ya faru domin bincike tare da tabbatar da bada tsaro ga al’ummar yankin.
Ya zuwa yanzu dai rundunar sojin saman ta ƙasa ba ta fitar da wani bayani kan lamarin ba, sai dai ana sa ran da zaran sun kammala bincike za su sanar da yadda lamarin ya kasance ga manema labaru.