Cutar daji ta yi ajalin shugaban Namibiya Geingob
Daga Sabiu Abdullahi
Shugaban Namibiya Hage Geingob, mai shekaru 82, ya rasu a asibiti da sanyin safiyar Lahadi.
Fadar shugaban kasar ce tabbatar da wannan labarin.
Wannan na zuwa ne makonni bayan da Geingob ya kamu da cutar daji.

