Cutar ƙyandar biri ta addabi nahiyar Afirka

Daga Sodiqat Aisha Umar
Hukumar yaƙi da yaɗuwar cututtuka ta Afirka ta ce nan ba da jimawa ba, za ta ayyana cutar ƙyandar biri da ta ɓarke a nahiyar, a matsayin wata matsala da ke buƙatar kulawar gaggawa.
Daraktan hukumar ya ce ya kaɗu da yadda aka samu ƙaruwar mutanen da ke ɗauke da cutar da kashi 160 cikin 100 a shekarar da ta gabata.
Wani nau’in cutar na yaɗuwa sosai a jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo inda cutar ta fi ƙamari.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ba da rahoton bazuwar cutar a sassan Afirka a wannan shekarar.
Ƙasashe 16 ciki har da Rwanda da Burundi da Uganda da Kenya duk sun sanar da ɓarkewar cutar.