November 8, 2025

Ciwon daji ya cafke tsohon shugaban Amurka Joe Biden

images - 2025-05-19T091348.258

Likitoci a birnin Washington DC sun bayyana cewa tsohon shugaban Amurka, Mista Joe Biden, na fama da cutar daji (cancer) wadda ta riga ta bazu zuwa ƙasusuwan jikinsa.

Biden, wanda ya sauka daga kujerar shugabanci kuma ya janye daga takarar wa’adin mulki na biyu, ya mika ragamar takara ga mataimakiyarsa Kamala Harris, wadda ta kware a fannin shigar da ƙara, bayan da likitoci suka gano yana fama da cutar mantuwa.

Tun bayan nasarar da Donald Trump ya sake samu a zaɓe, ba a ƙara ganin ko jin Biden a idon jama’a ba — sai yanzu da wannan rahoton ya fito daga bakin likitoci.