CIN AMANA: Yadda matashi ya hallaka ɗan uban gidansa saboda ba a kawo kuɗin fansa da wuri ba
Daga Sabiu Abdullahi
Akalla mutane hudu ne rundunar ‘yan sandan jihar Gombe ta gurfanar da su kan kisan wani matashi mai suna Alamin Ahmadu dan shekara 16.
Wadanda ake zargin sun hada da Ahmadu Ibrahim mai shekaru 25 da kuma Babuka Abubakar mai shekaru 35.
Sauran sun haɗa da Abdulsalam Mohammed mai shekaru 28 da Muhammadu Abubakar mai shekaru 28 da haihuwa, dukkansu a unguwar Liji da ke karamar hukumar Yalmatu Deba a jihar Gombe.
Da yake gabatar da wadanda ake zargin a ranar Juma’ar da ta gabata, jami’in hulda da jama’a na rundunar ASP Mahid Abubakar, ya ce rundunar da ke yaki da garkuwa da mutane ta samu korafi daga Ahmadu Yaya, mahaifin marigayin a Arawa quarters, cewa wasu da ba a san ko su wane ne ba ne sun kira su suka sanar da shi cewa sun yi garkuwa da dansa kuma suka bukaci naira miliyan 5 a matsayin kudin fansa.
A cewar Abubakar, Yaya ya kuma bayyana cewa dansa Alamin dalibin Ubaida Academy Arawa ne wanda ya bar gida domin yin wata sana’a.
Ya kara da cewa bai dawo ba har sai da aka yi masa waya ana neman a biya naira miliyan biyar.
Ya ci gaba da cewa, “Da samun wannan korafin, sashin yaki da garkuwa da mutane karkashin kungiyar O/C Anti Kidnapping ya dauki matakin kama wadanda ake zargin kuma nan take suka fara bincike. Wani bincike da aka yi ya nuna cewa daya daga cikin wadanda ake zargin mai suna Ahmadu Ibrahim, wanda ke aiki a wani kamfanin sarrafa shinkafa a karkashin mahaifin wanda aka kashe shi ne ya kitsa yin garkuwa da wanda aka kashe.
“Wanda ake zargin ya amsa laifin yin garkuwa da Alamin dan shekara 17 kuma ya kai shi tsaunin Lijji amma daga baya ya tabbatar da kashe shi sakamakon gazawar mahaifinsa ya biyan kuɗin fansa naira 700,000 kamar yadda aka amince a baya ta hanyar tattaunawa ta wayar tarho.
“Wadanda ake zargin. suna hannunmu kuma za a gurfanar da su a gaban kotu.”




