‘Ci gaba da ɗaga wa gwamnati ƙafa zai janyo hasarar rayuka’—shugaban NLC
Daga Sabiu Abdullahi
Shugaban ƙungiyar ƙwadago a Najeriya, Joe Ajaero, ya ce sun fito zanga-zanga ne a yanzu ganin cewa idan suka jinkirta yinta, mutane da dama na iya rasa rayukansu saboda tsananin halin matsi da jama’a na tsadar rayuwa.
BBC ta rawaito cewa Ajaero ya bayyana haka ne a yau yayin da ƙungiyar ke zanga-zangar yini biyu a ƙasar don nuna rashin jin daɗinta game da halin da ƙasar ke ciki.
Ya bayyana hakan ne a hirarsa da manema labarai a dandalin zanga-zangar a Abuja.
Ya ce shugabannin Najeriya sun tabbatar da yadda mutane suke cikin tsanani.
An ambato shi yana cewa, “Shi ne muke cewa idan aka ci gaba da haƙuri, to kowa na iya mutuwa kafin lokacin da za a yi wani abu, ku yi wani abu yanzu, shi ne kawai banbanci.
“Muna duba lokacin, muna son a yi wani abu cikin gaggawa kafin wata shekarar, dole mutane su rayu kafin su ji ci gajiyar aikin.”
Ya kuma ƙara da cewa yana da yaƙini cewa shugaba Tinubu zai yi wani abu game da halin da jama’a ke ciki.