China Za Ta Ba Wa Najeriya Rancen Euro Miliyan 245 Don Gina Layin Dogon Kano-Kaduna

Daga Sabiu Abdullahi
Bankin Raya Kasar China (CDB) ya amince da bayar da rancen Euro miliyan 245, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 254.76, domin tallafawa aikin gina layin dogo mai haɗa Kano da Kaduna a Nijeriya.
A wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Talata, ya bayyana cewa rancen zai taimaka wajen samar da kuɗin da ake bukata domin kammala aikin cikin lokaci.
Aikin zai kasance karkashin jagorancin Kamfanin Gine-gine na China (CCECC), wanda zai gudanar da shi tare da tallafin kuɗi daga CDB.
Sanarwar ta ce wannan rance zai inganta sufuri a Nijeriya, tare da bunkasa tattalin arziki da haɗin kai tsakanin jihohin biyu.
Layin dogon, mai tsawon kilomita 203, na da nufin samar da hanya kai tsaye daga Kano zuwa babban birnin kasar, Abuja.
“Haka kuma aikin zai bunkasa masana’antu, samar da ayyukan yi, da kuma sauƙaƙa harkokin sufuri ga ‘yan Najeriya,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa aikin yana cikin manyan shirye-shiryen da aka sa gaba a taron Belt and Road Forum karo na uku, wanda ke mai da hankali kan haɗin gwiwar tattalin arziki.
I regard something truly interesting about your site so I saved to fav.
Your point of view caught my eye and was very interesting. Thanks. I have a question for you.