Chelsea ta gama amincewa da sayen João Félix kan yarjejeniya ta dindindin daga Atletico
Daga Sabiu Abdullahi
Chelsea ta kammala yarjejeniya ta dindindin da Atlético Madrid don ɗaukar João Félix.
Dan wasan na Portugal na shirin komawa Stamford Bridge, inda a baya ya taka rawar gani yayin zaman aron da ya yi a can.
A cewar wasu majiyoyi, Félix zai yi gwajin lafiyarsa a Landan nan da awanni 48 masu zuwa kafin ya rattaba hannu kan kwantiragin shekaru shida da zai ci gaba da zama a Chelsea har zuwa watan Yunin 2030.
Yarjejeniyar ta kuma ƙunshi zaɓi don tsawaita zamansa har zuwa 2031.
Wannan yunƙurin wani bangare ne na yarjejeniyar musayar ‘yan wasa da za ta ga Conor Gallagher ya nufi Atlético Madrid.