CCB za ta binciki ministan cikin gidan Najeriya bisa zargin take doka
Daga Sabiu Abdullahi
A wani mataki na tabbatar da cewa ma’aikatan gwamnati sun yi abin da ya dace, Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikata ta Nijeriya (watau CCB a taƙaice) ta ce ta fara bincike a kan Ministan Harkokin Cikin Gida na kasar, Olubunmi Tunji-Ojo, “bisa zarginsa da take dokar ɗa’ar ma’aikata.”
Hukumar ta ce ta gayyaci ministan ya bayyana a gabanta a ranar Talata 16 ga watan Janairun 2024, a ofishinta da ke Sakatariyar Gwamnatin Tarayya a Abuja.
Wannan na ƙunshe ne cikin sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Litinin.
Ta ƙara da cewa ta aika masa gayyatar ne a bisa ikon da kundin tsarin mulkin Najeriya ya halatta mata.
Sanarwar ta ce, “Za a iya tuna cewa, a baya-bayan nan ministan ya shiga cikin kanun labarai kan zarginsa da take dokar ɗa’ar ma’aikata, bayan da Ministar Ma’aikatar Harkokin Jinkai da aka dakatar. ta bai wa wani kamfaninsa kwangila.”
Shin wannan za a iya cewa gwamnatin shugaba Tinubu tana ƙoƙari ke nan wajen yaƙi da cin hanci da rashawa a tsakanin jami’an gwamnati a Najeriya?