January 15, 2025

CBN ya yi gargadi wa jama’a saboda yadda jabun takardun naira suka yawaita

4
Old-and-New-Naira-notes-1140x570.webp

Daga Sabiu Abdullahi

Babban bankin Najeriya, CBN, ya gargadi ‘yan Najeriya da su yi hattara da kudaden Naira na bogi da ke yawo ba bisa ka’ida ba.

Wannan gargadi na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mukaddashin daraktan sadarwa na CBN, Hakama Sidi Ali, ta fitar a Abuja ranar Juma’a.

“An jawo hankalin Babban Bankin na CBN a kan yadda ake yada takardun kudi na jabu, musamman manyan kudaden da wasu mutane ke yi,” in ji ta.

Sidi Ali ya te jabun na Naira an fi amfani da shi wajen hada-hadar kasuwanci a kasuwannin abinci da sauran cibiyoyin kasuwanci a fadin manyan kasuwanni a garuruwan kasar.

Ta ce duk wanda aka samu da hannu wajen shigar da kudaden na jabu to zai fuskanci hukunci mai tsanani.Daraktar ta ce dokar ta tanadi hukuncin zaman gidan yari wanda ba zai yi kasa da shekaru biyar ba, ga duk wanda aka samu da laifin yin jabun kudin Naira ko kuma duk wata takardar doka a Najeriya.

“CBN na ci gaba da hadin gwiwa da hukumomin tsaro da wadanda suka dace domin kwato takardun kudin Naira na bogi, kamawa da hukunta masu yin jabun.”

“Ana kuma kara kira ga jama’a da su kai rahoton duk wanda ake zargin yana da kudin jabun naira ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa, reshen CBN, ko ta contactcbn@cbn.gov.ng,” in ji ta.

Daraktar ta ce dokar ta tanadi hukuncin zaman gidan yari wanda ba zai yi kasa da shekaru biyar ba, ga duk wanda aka samu da laifin yin jabun kudin Naira ko kuma duk wata takardar doka a Najeriya.

“CBN na ci gaba da hadin gwiwa da hukumomin tsaro da wadanda suka dace domin kwato takardun kudin Naira na bogi, kamawa da hukunta masu yin jabun.”

“Ana kuma kara kira ga jama’a da su kai rahoton duk wanda ake zargin yana da kudin jabun naira ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa, reshen CBN, ko ta contactcbn@cbn.gov.ng,” in ji ta.

4 thoughts on “CBN ya yi gargadi wa jama’a saboda yadda jabun takardun naira suka yawaita

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *