CBN ya janye dokar hana amfani da kuɗin kirifto
Daga Sabiu Abdullahi
An samu wani gagarumin sauyi na manufofin kuɗi yayin da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya janye dokar hana hada-hadar kudi na kirifto (watau cryptocurrency a Turance).
Bankin ya fitar da sabbin ka’idojin da ke maraba da masu ba da sabis na kadarorin yanar gizo cikin tsarin hada-hadar kudi.
Wata sanarwa, wadda aka fitar ranar Juma’a mai lamba FPR/DIR/PUB/CIR/002/003, ta amince da yanayin da ake ciki a duniya game da kadarorin yanar gizo kuma ya jaddada bukatar samun “ka’ida don hana yin amfani da kadarorin yanar gizo wajen satar kudi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci.”
Idan ba a manta ba, a baya dai bankin na CBN ya bayyana damuwarsa kan rashin daidaiton kudi, rashin tsari, da yiwuwar aikata laifuka a matsayin dalilan da suka sanya aka sanya dokar hana amfani da kuɗin kirifto.