CBN ya buƙaci masu canjin kuɗi su sabunta lasisinsu kafin ƙarshen 2024
Daga Sodiqat Aisha Umar
Babban bankin Najeriya, CBN ya buƙaci masu musayar kuɗi a ƙasar nan, da su sake neman buƙatar sabunta lasisinsu.
Cikin wata sanarwa da Babban Bankin ya fitar ranar Laraba, ya ce ya ɗauki matakin ne domin daidaita kasuwar musayar kuɗi don bunƙasa harkokinsu.
CBN ɗin ya ce a yanzu mafi ƙarancin jarin da masu musayar kuɗi ya kamata su mallaka shi ne naira biliyan biyu ga ‘yan rukunin farko na Tier 1, yayin da ‘yan rukuni na biyu watau Tier 2 zai koma naira miliyan 500.
Haka kuma sabuwar ƙa’idar da CBN ɗin ya fitar ta soke kuɗin ajiya na dole da masu rukunin farko suke ajiyewa na dole na naira miliyan 200, da kuma naira miliyan 50 na masu rukuni na biyu.
Cikin Sanarwar da CBN ya aike wa masu chanjin kuɗin, ta nuna cewa sabuwar dokar za ta fara aiki daga ranar 3 ga watan Yuni.
CBN ɗin ya kuma bai wa masu musayar kuɗin wa’adin mako shida da su cika waɗannan sharuɗa