February 12, 2025

CBN ya ƙara kuɗin da bankuna ke buƙata a matsayin jari zuwa naira miliyan 500

197
images-1-15.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Babban Bankin Najeriya (CBN), ya kara adadin kuɗin da bankuna za su iya mallaka a matsayin jari zuwa maira biliyan 500.

Wannan sanarwar na kunshe ne cikin wata takardar da daraktan sashen tsare-tsare da sanya ido kan ka’idojin kudi, Haruna Mustafa, ya sanya wa hannu.

A cewar CBN, dole ne kowane banki da ke hada-hada har a ƙasashen ƙetare ya kasance yana da jarin da bai gaza Naira biliyan 500 ba.

CBN, ya bai wa bankunan kasuwanci da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi wa’adin watanni 24 domin cika wannan ka’ida.

Wannan wa’adi zai fara aiki daga ranar 1 ga watan Afrilu, 2024, zuwa watan 31 ga Maris, 2026.

Bankunan da hada-hadarsu iya Najeriya ta tsaya, na buƙatar mafi ƙarancin jari na Naira biliyan 200 domin cikar ka’idar da CBN ya gindaya.

197 thoughts on “CBN ya ƙara kuɗin da bankuna ke buƙata a matsayin jari zuwa naira miliyan 500

  1. Где и как купить диплом о высшем образовании без лишних рисков

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *