January 13, 2025

Burkina Faso ta fito da sabon fasfo da babu tambarin ECOWAS a jikinsa

0
images (11) (9)

Daga Sabiu Abdullahi  

Burkina Faso ta ɗauki wani muhimmin mataki na karfafa ficewarta daga kungiyar ECOWAS, ta hanyar bullo da sabbin fasfo na zamani wadanda ba su da tambarin kungiyar.  

A wajen kaddamar da taron a ranar Talata, ministan tsaro Mahamadou Sana ya bayyana cewa, “A kan wannan fasfo, babu tambarin kungiyar ECOWAS, haka nan ma ba a ambaci kungiyar ECOWAS ba.” 

Tun daga watan Janairu, Burkina Faso ta yanke shawarar janyewa daga wannan ƙungiya, kuma wannan shi ne kawai fahimtar matakin da Burkina Faso ta riga ta ɗauka.”  

Wannan matakin ya kara karfafa aniyar Burkina Faso na yanke hulda da kungiyar ECOWAS mai mambobi 15 a yankin.  

Kungiyar ECOWAS ta yi gargadin cewa ficewar kasashen Burkina Faso da Nijar da Mali daga kungiyar zai haifar da sakamako mai yawa, wanda hakan zai kawo cikas ga ‘yancin walwala da kuma daidaiton kasuwar bai-ɗaya da ‘yan kasa miliyan 400 na shekaru 50 za su amfana.

Wannan na zuwa ne a wani muhimmin lokaci, a daidai lokacin da kasashen uku ke kokawa kan barazanar da kungiyoyin ‘yan tayar da ƙayar baya masu alaƙa da al-Qaeda da IS ke yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *