January 24, 2025

Bunkasa arziƙi: ‘Ku koma amfani da kayayyakin da ake samarwa a Najeriya, maimakon na waje’

0
01-rice.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Tsohon mai magana da yawun tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya koka kan yadda Najeriya ke kashe maƙudan kuɗaɗe yau da kullum kan shinkafar ƙasashen waje, inda ya nuna saɓanin ra’ayi game da yadda ake raba kuɗi wa muhimman sassa kamar kiwon lafiya da ilimi.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter (watau X) a jiya, Omokri ya jaddada cewa Najeriya na kashe zunzurutun kudi har biliyan 2.3 a kowacce rana wajen sayen shinkafar da ake shigowa da ita daga ƙasashen waje, wanda ya zarce kuɗaɗen da ake sakaws a fannoni masu muhimmanci kamar kiwon lafiya da ilimi.

A sakon da Omokri ya wallafa a shafinsa na twitter ya haifar da cece-kuce kan abubuwan da al’ummar kasar suka sa a gaba, tare da nuna shakku kan dorewar kashe kuɗaɗe masu yawa kan shinkafar da ake shigowa da ita daga ƙasashen waje tare da yin watsi da muhimman sassa masu muhimmanci ga ci gaban ƙasa.

Da yake nuna damuwarsa kan yadda ake rabon albarkatun ƙasa, ya yi tambaya kan wajabcin amfani da shinkafar waje a lokacin da ake da zaɓi na cikin gida.

Saƙon ya nuna yadda Najeriya ke dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje, inda ya bayyana yadda ake kashe dala miliyan 10 a kullum kan ayyukan da kamfanoni na kasa da kasa kamar MTN, DSTV, da Shoprite ke yi.

Omokri ya bukaci ‘yan Najeriya da su rungumi kayayyakin da ake samarwa a cikin gida a matsayin wata hanya ta bunkasa tattalin arzikin kasar da kuma bunƙasa dogaro da kai.

Da yake kwadaitar da ‘yan kasa su mallaki kayayyakin Najeriya, Omokri ya gabatar da wasu tsare-tsare irin su tallafa wa kamfanonin shinkafa na Kebbi da Abakaliki, burodin rogo, amfani da kamfanin sadarwar gida kamar Glo, tuƙa motocin da Innoson Motors ke kerawa, da cin taliyar Dangote.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *