Buba Galadima ya karyata jita-jitar komawar Kwankwaso APC

Jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya nesanta tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a zaben 2023, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso, daga jita-jitar da ke yawo cewa yana shirin komawa jam’iyyar APC.
Galadima ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP ta riga ta ba ‘yan Najeriya damar fahimtar irin nagartaccen shugabanci da za ta iya bayarwa, wanda ya ginu a kan gaskiya da rikon amana.
Ya ce babu wani shiri na sauya sheka daga Kwankwaso, kuma wannan jita-jita ba ta da tushe.
A baya-bayan nan ne shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya yi hasashen cewa Kwankwaso zai koma jam’iyyar APC, inda ya ce tsohon dan takarar shugaban kasar yana shirin komawa jam’iyyar.
Ganduje ya bayyana hakan ne a lokacin da yake karbar bakuncin wasu magoya bayan shugaban kasa Bola Tinubu a Abuja, yana mai cewa jam’iyyar APC na ci gaba da jawo manyan ‘yan siyasa ciki har da ‘yan majalisar tarayya, kuma suna dakon dawowar Kwankwaso cikin jam’iyyar.