February 10, 2025

Breketa Family sun tsagaita da yaɗa shirye-shirye don nuna damuwa kan musguna wa ƙananan yaran

0
IMG-20241104-WA0011.jpg

Daga Abdullahi I. Adam

Mamallakin gidan yaɗa labarun nan mai rajin kare haƙƙin al’umma Ahmed Isah wanda aka fi sani da Ordinary President ya sanar da cewa za su tafi hutu gami da daina gudanar da ayyukansu na ɗan wani lokaci.

Kamar yadda ya bayyana, Ahmed Isah ya ce wannan mataki ya zama tilas domin wannan wani yunƙuri ne na nuna ma mahukunta ɓacin ransu kan irin yadda aka ci zarafin wasu ƙananan yara masu yawa waɗanda aka kama sanadiyyar zanga-zangar tsadar rayuwa da aka gabatar.

A cikin bayanin da ya yi, Ahmed ɗin ya bayyana cewa abinda aka yi wa yaran “take haƙƙinsu ne” sannan ya yi kira da a gaggauta sakin yaran.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *