January 14, 2025

Brazil ta rufe gidajen caca na intanet sama da 2,000

0
20_47_03_images.jpg

Daga Sabiu Abdullahi

Gwamnatin Brazil ta ɗauki matakin gaggawa don shawo kan caca ta yanar gizo ta hanyar rufe sama da gidajen caca na intanet 2,000, waɗanda suka haɗa da masu ɗaukar nauyin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa da suka shahara kamar Corinthians da sauran kulob-kulob.

Wannan matakin na cikin yunƙurin gwamnatin Shugaba Luiz Inacio Lula da Silva na yaƙi da damfara, zamba, da kuma kare masu amfani da shafukan.

Ministan kuɗin Brazil, Fernando Haddad, ya bayyana cewa ƙasar na fama da wata irin “annobar” caca, lamarin da ya sa gwamnatin ta ɗauki matakin ƙara tsauraran dokoki kan wannan fanni.

Sabbin dokokin, waɗanda za su fara aiki daga watan Janairu, sun haramta wa ƙananan yara yin caca kuma sun wajabta wa gidajen caca yin rajista da gwamnati.

Ma’aikatar kuɗi ta gano gidajen caca har guda 2,040 waɗanda ake zargin ba su da tsari, sannan kuma sun nemi hukumar sadarwa ta Anatel ta rufe su.

Gidajen da ba su bi doka ba za a hana su talla da ɗaukar nauyin kulob din ƙwallon ƙafa. Duk da haka, gidajen caca fiye da 200 da suka amince da sabbin dokokin za a bar su su ci gaba da aiki.

Babban bankin Brazil ya kiyasta cewa mutane miliyan 24 daga cikin miliyan 212 na mazauna ƙasar, kusan mutum ɗaya cikin tara, suna yin caca ta yanar gizo.

Shugaba Lula ya gargadi cewa caca na sa masu ƙaramin kuɗi shiga cikin bashi.

“Waɗanda ba su da rajista ko kuma ba sa kan hanyar yin rajista, za a cire su daga kan tsari,” in ji Haddad.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *