February 10, 2025

Borno: Ƴanta’adda Sun Ƙona Coci da Gidaje

1
images-2.jpeg

Daga Sabiu Abdullahi

Mayaƙan Boko Haram sun kai hari a garin Shikarkir, dake ƙaramar Chibok a jihar Borno, inda suka ƙona wani coci da gidajen mutane. Wannan harin ya biyo bayan wani hari da suka kai a ƙauyen Bazir, inda suka kashe mutum biyu sannan suka ƙona wani cocin.

Kakakin rundunar ƴansandan jihar Borno, ASP Nahum Daso, ya tabbatar da harin a ƙauyen Bazir yayin tattaunawarsa da manema labarai. Sai dai ya ce bai samu bayani kan harin na Shikarkir ba.

Daniel Shikarkir, wanda aka ƙona masa gida, ya bayyana cewa, “Kafin su kai wannan hari, sun kai irin wannan harin a ƙauyen da ke kusa da mu. Yanzu haka, mutanen garin suna gudun hijira, suna neman mafaka a wasu wurare.”

1 thought on “Borno: Ƴanta’adda Sun Ƙona Coci da Gidaje

  1. I like thhe vasluable info youu provide iin yoir articles.

    I will bookmark your weblog aand chck again ere regularly.
    I’m quite certainn I’ll learn plentyy oof nnew sfuff right
    here! Goodd luck forr thhe next!

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *