Boko Haram ta kai wa manoma hari a Borno
Daga Sadisu Salisu
Rahotannin da suke shigo mana daga Arewa maso Gabas ɗin Najeriya na nuna cewa maharan Boko Haram sun kai wa manoma hari.
Majiyoyi sun ce yan Boko Haram ɗin sun yi wa manoman ƙawanya ne a lokacin da suke tsaka da girbi a kauyukan Karkut da Koshebe dake karamar hukumar Mafa.
Zuwa yanzu, rundunar yan sa-kai ta ce ta gano gawarwakin manoman 13, sannan suna ci gaba da neman wadanda suka bace.
A baya-bayan nan gwamnan jihar, Babagana Zulum, ya ce babu ko yanki guda da ya rage a ƙarƙashin ikon Boko Haram.
A halin yanzu dai yawancin wadanda rikicin ya kora suna dawowa muhallansu.