Bikin Sallah: Limami ya ja hankalin hukumomi
Daga Abdullahi I. Adam
A huɗubar da ya gabatar bayan kammala sallar idin da ya gudana da safiyar nan, Imam Khamis Dalhatu da ke Shika-Zaria, ya nemi hukumomi da su nemi hanyoyin daƙile harkar shaye-shaye da rashin tarbiyya da suka zame ruwan dare a cikin al’umma.
Limamin ya faɗakar da shuwagabanni cewa tabbas Allah SWT zai tambaye su kan irin salon jagorancin al’umma da ke rataye a kansu.
Kafin isowar limamin, Ustaz Ahmad Sirajo ya gabatar da nasiha a filin Idin, inda shi kuma ya maida hankali kan faɗakar da jama’a cewa irin tarbiyya da suka samu yayin azumin watan Ramadan bai kamata su yi watsi da ita ba.
Malamin ya tunatar da mahalarta sallar cewa saɓon da Allah SWT Ya haramta cikin watan na Ramadan irinsa ne dai aka hana bayan azumin, don haka wajibi ne ga kowa ya kiyaye dokokin Ubangiji Kamar yadda su ke.
Daga ƙarshe limamin ya ja hankalin iyaye da su sa idanu matuƙa don tabbatar da cewa yara ba su aikata halaye marasa kyau a yayin gudanar da shagulgulan sallar idin na wannan karo ba.
Jama’a da dama da muka zanta da su bayan kammala sallar, sun nuna jin daɗi da farin ciki ganin yadda ake ta gudanar da shagulgulan sallar cikin godiya da Ubangiji musamman ganin cewa yankin ya soma samun sauƙin matsalar tsaro da yayi ta fama da ita a baya.
An yi addu’o’i da fatan alkhairai ga ƙasa da kuma Jihar Kaduna bayan kammala sallar.
Allah Ya dafa mana.