January 24, 2025

Bello Turji yana cikin tsananin tsoro saboda sabbin farmaƙin da sojoji ke kaiwa—Christopher Musa

0
images (12) (16)

Daga Sabiu Abdullahi  

Shugaban Hedikwatar Tsaro (CDS) na Najeriya, Janar Christopher Musa, ya ce babban jagoran ‘yan ta’adda da ake nema, Bello Turji, yana cikin tsananin tsoro sakamakon sabon farmakin sojoji a kan ‘yan ta’adda a Arewa maso Yamma. 

Musa ya bayyana hakan ne a wata hira da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a gefen taron farko na NAN na Bikin Laccar Duniya da aka gudanar ranar Alhamis a Abuja. 

Mista Musa ya bayyana cewa kisan Halilu Buzu da wasu shugabannin ‘yan ta’adda da dama ya haddasa tsoro a sansanin Turji da tawagarsa, yana mai cewa ayyukansa na baya-bayan nan suna nuna alamar tsoro. 

“Za ka iya gani daga ayyukan da yake yi; za ka gane cewa yana cikin halin tsoro. 

“Kafin haka, yana da karfin gwiwa yana fita yana magana kamar shi kadai ne yake iko da komai. 

“Yanzu ya gane ba shi da iko. Ya gane cewa lokaci ne kawai, domin Halilu Buzu da aka kashe shi ne ubangidansa. 

Har yanzu dai lamura suna nan rincaɓe a Arewa maso Yammacin Najeriya inda ake ci gaba da kashe tare da sace mutane domin kudin fansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *