January 15, 2025

Bayani game da lamarin cutar damuwa (Depression)

42
IMG-20240322-WA0021.jpg

Daga Jaafar A Sarki

Akwai nau’in cututtuka daban-daban da ɗan Adam ke gamuwa dasu a wannan rayuwa.

Wasu sun kasance masu yaɗuwa daga mutum zuwa mutun (communicable diseases), kamar HIV, Covid, TB, dss.

Wasu ba sa yaɗuwa (non-communicable diseases), kamar, Cancers, cututtukan zuciya Cardiovascular diseases), cutar Sikari (Diabetes), dss.

Daga cikin cututtakan da mutum kan kamu da su akwai waɗanda suka fi samuwa a yankunan ƙasashen dake da zafi (tropical and subtropical dieases), akwai kuma waɗanda suke a yankin ƙasashe masu sanyi (temperate diseases), sannan akwai kuma cututtukan da duk inda mutum yake a duniya suna tare dashi, wato mutum kan iya kamuwa da su, ana kiran su da ‘Global diseases’.

Akwai kuma waɗanda su lafiyar kwakwalwa suke tabawa kawi, to daga cikinsu akwai ‘Depression’ wanda ya kasance ɗaya daga ‘Global diseases’ wanda ko wane mutum kan iya fama dashi a duk inda yake a faɗin yakan duniya.

Shi mutum yana da ’emotion, a tare dashi wato yakan ji farin ciki (happiness) yakan ji haushi sannan yakan samu kansa cikin bakin ciki (sadness).

Haka  ’emotion’ ɗin mutum ke samun canji daga lokaci zuwa lokaci kuma jin hakan ba matsala bane a tare da mutum.

Amma inda kan iya zama matsala shine idan damuwa ta zaunawa mutum ‘constantly’ a zuciyarsa, to jin hakan shi ke rikiɗewa ya zama ‘Depression’.

Shi ‘Depression’ ya kasance lalura ce dake tattare da bayyanar alamomin na ‘”sadness, hopelessness, loss of interest in usual activities, fatigue, poor concentration, and other negative thoughts, feelings and other physical symptoms that interfere with normal daily activities.

Kamar yadda Jacobsen ya bayyana cikin littafinsa mai suna “Introduction to Global Health”.

A kowace shekara mutum ɗaya cikin biyar na fuskantar Depression’ a faɗin duniya musamman a tsakanin matasa, kamar yadda ya sake bayyanawa.

‘Depression’ kan jawo matsaloli ga ma’abocinsa, ta fuskar ayyukansa da tunaninsa.

Mutum kanji bashi da wani hope ko amfani ga rayuwarsa ko ga waninsa dan haka ma wasu har na iya tunanin kauda samuwarsu ta hanyar hallaka kansu su huta da bakin cikin rayuwa.

Amma fa duk da yadda yakai ana iya samun nasarar rabuwa dashi, har mutum ya koma ayyukansa na yau da kullum ba tare da jin irin wannan damuwar ba, kuma ya zama kamar bai yi ba.

Masana wannan lalurar na cewa ana iya magance ta da low-cost medications da psychotherapy wato “cognitive behavioural therapy” (CBT).

Shi ‘CBT’, hanya ce ta magance wa mai depressive disorder lalurarsa ta tattauna dashi domin fahimtar ‘thoughts da feelings, da halaye da dabi’unsa domin gano matakan da za’a dauka domin magance masa matsalolinsa dashi wannan ‘Depression’ ke haddasawa mutum.

Allah ya bawa masu fama da wannan larura lafiya mu kuma Allah ya kare mu.

42 thoughts on “Bayani game da lamarin cutar damuwa (Depression)

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *