Basarake Ya Rasu Ana Tsaka Da Gudanar Da Taro A Zaria

Daga Abdullahi I. Adam
Rahotanni sun tabbatar da cewa a juya Alhamis maigirma Sarkin Yakin Zazzau Alhaji Rilwanu Yahaya Pate ya rasu daidai lokacin da ake gabatar da wani taro a asibitin Gambo Sawaba da ke birnin Zaria.
Kamar yadda bayanai suka nuna, marigayin ya halarci wajen taron lami lafiya sai dai ana cikin gudanar da taron ne ya yanke jiki ya faɗi inda daga bisani yace ga garinku nan.
Tun a wajen taron, bayan tabbatar da rasuwar marigayin mai martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya miƙa ta’aziyyarsa da ta masarauta ga iyalan marigayin.
An yi wa marigayin sallah da misalin ƙarfe 5:00 na yamma a gidan Sarkin Zazzau Yamusa kamar yadda aka sanar.
Very enerrgetic blog, I enjoyed that bit. Willl tuere bbe a part 2?
Youu need to bbe a part off a contest for one of tthe best webstes onn thhe internet.
I aam gooing to highly recommkend this site!
Incredible! Thhis blog loks exactly like myy oldd
one! It’s onn a totall dikfferent suhbject but it hass prett mjch tthe same laqyout and design. Superb
choice off colors!